Labaran YauLabaran Bauchi

Zamu Cigaba Da Haɗin Gwiwa Da Jami’o’i Don Yaki Da Munanan Ayyuka- Gwamna Bala

Zamu Cigaba Da Haɗin Gwiwarmu Da Jami’o’i Don Yaki Da Munanan Ayyuka, Gwamna Ya Samu Ganawa Da Majalisar Gudanarwa na Fed. Uni Azare, ATBU.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya jaddada wajabcin hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki da gwamnatoci a dukkan matakai domin dawo da cibiyoyin ilimi da manhajoji domin ci gaban al’umma.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shuwagabannin jami’ar lafiya da kimiya ta tarayya wanda ke cikin garin Azare na Abubakar Tafawa Balewa University Bauchi, a yau a gidan gwamnatin Bauchi.

Gwamna ya bayyana damuwarsa game da rashin aikin yi da matasa ke fuskanta, yana mai cewa za a iya rage wadannan ta hanyar sabunta manhajar karatu ta yadda za a samu ci gaban fasahar zamani.

A cikin jawabansu daban daban, wakilan jami’o’in gwamnatin tarayya sun yabawa Bala Mohammed bisa manufofi da tsare-tsare da gwamnatinsa ta bullo da su da suka shafi matsalolin rashin makaranta da sauransu, inda suka ba shi tabbacin ci gaba da bayar da goyon baya ga al’umma.

Ga kadan daga cikin hotunan da aka dauka a wajen taron daga bisani ⇓

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button