Labaran Yau

Rahoto Ta Bayyana Mutane Miliyan 258 Suka Fada Yunwa A…

Rahoto Ta bayyana miliyan 258 suka fada yunwa a duniya

Yawan mutanen da yunwa ta shafa ya haura a shekarar 2022, a binciken kungiyoyin kasashen duniya, kungiyar tarayyar turai da kuma wasu hukumomi da ke karkashin Majalisan dinkin duniya.

A yanda jami’in Labaranyau ya samo rahoton, wanda aka bayyana ran laraba, ta bayyana cewa sama da kwatan biliyan na mutane ke cikin matsanancin yunwa saboda annoba na yunwa data bayyana a shekarar 2022.

Daban da shekarar 2021, yawan mutanen sun kasu kashi uku wanda rashin abinci ke addabarsu, sun karu daga miliyan 193 zuwa miliyan 258.

DOWNLOAD ZIP/MP3

A bayanin rahoton, matsalolin na fadace fadace wanda ya shafi wasu nahiyoyi, da yaduwar cutar corona virus, da Kuma yakin Rasha da yukrain, Suna daga cikin matsaloli da suka haddasa yaduwar yunwa a duniya.

Duk cikin rahoton, an samu gudumawar daga Majalisan dinkin duniya na reshen abinci da kayan gona da kuma shirin abinci ta Majalisan dinkin duniya WFP.

“Sama da kwatan biliyan na mutane Suna fuskantar matsanancin yunwa wasu Kuma Suna cikin yanayi na rashi gaba daya” Sakatare janar na Majalisan dinkin duniya Antonio Guterres ya rubuto a rahoton cewa hakan baiyi kyau ba.

“Yawan mutane da matsanancin yunwa ya shafesu na rashin abinci ta bayyana hoton tausayi” cewar Rein Paulsen, daraktan Abinci da kayan gona.

Mutum miliyan 258 ya annoban ya shafa, “gidanjen da basu da hali, wanda rayuwa da rayuwarsu ta ke cikin mawiyacin hali”.

Matsanancin hali da rashin abinci Ana dubawa ne a sikeli wanda ta nuna mutane suna shan wahala sosai.

Rahoto ya nuna mutum miliyan 35 Suna cikin matsanancin hali na taimako a shekarar 2022.

Kuma a cikin rahoton ta nuna an samu mutum dubu dari uku da saba’in da shida sun kai matakin matsanancin hali na yunwa.

Masana sun bayyana cewa a hakan ma ba a hada duka yawan mutanen ba.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button