Labaran Yau

Kasar Britaniya Na Daf Da Aika Alison Madueke Gidan Yari Bisa Zargin Cin Hanci

Labaran da muka samu daga kasar Britaniya sun tabbatar da cewa, ‘yan sandan kasar Britaniya sun ce suna tuhumar Madueke ne da laifin karbar cin hanci, inda suka ce suna zargin ta karbi cin hanci a matsayin ta na bayar da kwangilolin man fetur da iskar gas na fam miliyan.

Alison-Madueke, mai shekaru 63, ta kasance jigo a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Ta taba rike mukamin ministar mai daga shekarar 2010 zuwa 2015 sannan ta rike mukamin shugabar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC.

“Muna zargin Diezani Alison-Madueke ta yi amfani da ikonta a Najeriya kuma ta karbi tukuicin kudi don bayar da kwangiloli na fam miliyan,” in ji Andy Kelly, Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (NCA).

“Wadannan tuhume-tuhumen wani ci gaba ne a cikin abin da ya kasance cikakken bincike na kasa da kasa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button