Labaran Yau

Kotu Ta Hana Dan Kasar Netherland Dake Bada Maniyyi Dan Haifan

Kotu ta hana dan kasar Netherland dake bada Maniyyi dan haifan yara a duniya

Karamin kotun gunduma na garin Hague, a kasar Netherland ta dakatar da wani Mai shekaru 41 na bada maniyyi bayan an haifi yara 550 da hamsin daga jikin shi a fadin duniya.

Mutumin Mai suna Jonathan M, zai iya biyan taron kudin yuro dubu dari in ya karya dokar da kotu ta gindaya Mai.

DOWNLOAD MP3

A bayanin BBC, kotu a shekarar 2017 ta dakatar dashi daga bada maniyyi bayan an haifi yara dari daga jikin shi kasar Netherland. Sai ya koma bada wa a ta yanan gizo da wasu kasashen duniya.

Kotun ta bada umarnin ya kawo sunayen asibitocin da ya ke bada maniyyi saboda a halaka wanda ya bayar.

Mutumin ya kasance mai yaudaran mata dayawa, Kuma dokar kasar ta amince da mutum zai iya bada maniyyi wa ahali goma sha biyu Kuma zai iya haifan yara ashirin da biyar ne kawai.

DOWNLOAD ZIP

Alkali mai shari’a Thera hassellink tace ya bada maniyyi aka haifi yara 550 zuwa dari shida tun lokacin da ya fara badawa a shekarar 2007.

Gidauniyar dake kare yancin yara da aka haifa wajen karbar maniyyi ne takai karar kotu da Kuma daya daga cikin uwar da ta haifi da daya daga maniyyinsa.

Yara sama da dari aka haifa da maniyyinsa a wata asibitin Denmark, wanda suka rarraba adireshin su zuwa kasashe daban daban.

Hesselink ya kara da haramta mai bayarwan da cigaba da bada maniyyinsa.

Kuma haramta shi da kiran iyaye dan tallata bada maniyyi ko ma wasu kungiyoyi.

Mutumin yayi karyan yawan maniyyinsa wa iyayen da suka karbi maniyyinsa kotun hague tace.

“Iyayen sun kasance cikin rudanin haihuwar da daga jinin mutum daya da yan uwa masu yawa wanda yaran basu zabi hakan da kansu ba” a fadin su.

Kotun tace hakan zai iya kawo haramtattun dabi’u wa yaran Kuma Suna Jan kunne da hana bada maniyyin wa mutane dayawa.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button