Ramadan: Saudi ta bada Abinci wa Yan Gudun hijira a borno
Hukumar Jin kai da taimako na Sarki Salman daga Saudi Arabia, KSrelief, ta baiwa gidaje masu rauni sama dubu biyar da dari uku kayan abinci a borno dan watan ramadana.
A wajen rarraba abincin a masaukin masu rauni wanda keh Muna a maiduguri ranan Litinin da ta gabata, darakta janar na NEMA, Mustapha Habib, ya yaba cibiyar wajen isar da hanun taimako wa kasar Najeriya a kawoni yanayi data tsinci kanta.
Habib, wanda Abdullahi Adamu ya wakilce shi, maitaimakin darakta ne na tsare tsare, bincike da tsinkaya NEMA.
Ya bayyana cewa wannan raba abinci yazo ne a daidai lokacin da ake bukata a watan ramadana.
“Cibiyar KSrelief ta yi kyautar abincin ne ta hanun NEMA, wanda suke rarrabawa yau wa gidaje dubu biyar da dari uku masu rauni wanda suka fuskanci jarabawa ta yan ta’adda a jihar.
“Masu raunin suna cikin ragistar NEMA wanda aka samun hadin kan hukumar tasu ta jihar borno SEMA dan isar dasu”. Inji Habib.
A cewarsa koh wani gida zata samu 59kg na abinci, shinkafa 25kg, wake 25kg, garin tuwo ta masavita 4kg. Tumatiri 2kg, man gyada lita biyu gidd da gishiri 1kg da maggi 0.8kg.
Duba da hadakayyar su tsakanin NEMA da cibiyar tun 2018 zuwa 2021, cibiyar ta bada gudumawa na kayan matsarufi wa masu rauni a Borno, yobe da zamfara wanda hakan ya taimaka wajen ceton rayuka a jihohin.
A madadin gwamnatin borno, darakta ta bincike da kididdiga ta SEMA, Ali Isa, ya yabi taimakon wanda tazo kan lokaci wajen taimakawa jihar.
Masu rauni da sukayi magana a taron, sun bayyana godiyansu wa Allah, da gwamnatin saudiya da kuma Duk wanda suka taimaka wajen isar abincin garesu a wannan wata meh tsarki na ramadan.