Labaran Yau

Gwamna Radda Yana Da Shirin Daukan Malamai 7000 Wa Makarantun Gwamnati

Gwamna Radda Yana Da Shirin Daukan Malamai 7000 Wa Makarantun Gwamnati

Gwamnatin Jihar katsina ta ce tayi shirin daukan aiki na malamai 7000 a makarantu na kananan hukumomi na gwamnati na jihar.

Mai magana da yawun gwamna Dikko Radda, Ibrahim Kaula ya bayyana hakan a Jawabin da yayi ranan Asabar.

Kaula ya bayyana cewa mataimakin gwamna Faruk Jobe ya fadi hakan wajen rantsar da kwamitin daukan aikin.

Jobe ya kara da cewa gwamnatin jiha ta shirya jarabawan daukan aiki wa malaman S-Power wajen mai dasu Malaman gwamnati a tabbatar dasu cikin aikin koyarwa.

A bayanin shi, A kalla malamai 5000 suke da Diploma da NCE Kuma 2000 daga ciki Suna da degree wanda suke koyarwa a firame da Sakandare karkashin S-power a jihar gabadaya.

Mista Jobe yace an kawo tsarin ne wajen tabbatar da ingancin ilimi wanda gwamnati ta kawo.

“Anyi hakan ne dan kawo malaman da suka kware wajen bada ilimi Mai inganci dan gyara zamanin gaba wa daliban jihar.”

Ya jaddada duba da Yana yin daukan aikin da akayi karkashin Hukumar Subeb ta jihar inda aka dauki Malamai 3889.

“Wannan sabbin daukan sai sunbi tsarin daukan malami inda Sai mutum ya rubuta jarabawa yaci dan tabbatar da an dauki kwararrun malamai dan ingancin ilimi” Ya ce.

Mataimakin gwamnan yace hanyoyi masu inganci za a bi wajen tantance malamai da gaskiya da kima.

Sakataren Gwamnatin jiha Ahmad Dangiwa, ya bayyana wa kwamitin cewa suyi aiki da Gaskiya tsakani da Allah babu rashin gaskiya.

Jagoran Kwamitin Sabiu Dahiru da sakataren Lurwanu Gona, an basu sati hudu wajen tattara rahoto su mika.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button