Labaran Yau

Majalisan Dattawa Ta Bayyana Masu Daukan Nauyin Gyaran Hanyan Jirgin Kasa na Kano – Kaduna

Majalisan Dattawa ta bayyana masu daukan nauyin gyaran hanyan jirgin kasa ta Kano-kaduna

Majalisan dattawa ran talata ta bayyana wanda zasu dau nauyin gyaran jirgin kasa daga kano zuwa kaduna.

tsoffin masu daukan nauyin, bankin shiga da fita ta kasar sin, ta janye daukan nauyin, ta baiwa bankin ci gaba ta sin kofar daukan nauyin.

Zuwa yau, majalisan dattawa ta daidaita dokar cin bashin gwamnatin tarayya ta shekara 2016 zuwa 2018 don sabonta aikin.

Kudirin ta biyo ne bayan Sanata Sadiq Umar daga jihar kwara ya bayyana.

Sanata Umar ya bayyana cewa majalisan dattawa ta amince wa cin bashin biliyan 22.8 na dalar Amerika don sabonta aikin hanyar jirgin kasa a shekarar 2020.

Ya kara da cewa an amince da hakan, yiwuwar hakan tayi wuya bayan ibtila’in Cutar Covid-19 wanda ta bayyana hakan yasa bankin sin ta gida da waje ta dakatar da aikin.

Don yin aikin, yan kwangilar kampani masu kerakere (CCEC) da kuma ministirin zirga zirga ta tarayya sukayi hadakayya dan samun bankin cigaba na kasar sin kuma suka amince da bada kudi dala miliyan dari tara da saba’in da uku da digo biyar.

Sanatoci daga ciki sunyi korafi kan koh an bada kudaden masu yawa na farko? Saboda kudin yayi yawa. Sanata jibrin isa ya bayyana cewa yakamata Ana lura da kyau akan kudade.

Shugaban kwamitin majalisan dattawa kan basussukan waje da cikin gida. Sanata Clifford Ordia yace dala biliyan Ashirin da biyu na ayyuka daban daban guda biyar ne.
Kuma sauran ayyuka an amince dasu Banda na Kano zuwa kaduna.

A bayanin shugaban Majalisan Dattawa, Ahmed Lawan, yace lamarin ta fara faruwa ne 2018 Kuma Mun amince a 2020.

“ Ba magana muke akan amincewar bashin ba, masu bada kudin aikin ne suka janye, Kuma mun samu masu badawa yanzu” a cewar sa.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button