Labaran Yau

Mutum Dubu Bakwai Da Dari Takwas Neh Aka Samesu Da Cutar Tarin Fuka A Jahar Bauchi

Mutum dubu bakwai da dari takwas aka samu da tarin fuka a jahar Bauchi

A Jahar Bauchi an samu mutum dubu bakwai da dari takwas da shida masu cutar tarin fuka a shekarar dubu biyu da Ashirin da uku da ta gabata, hakan ya bayyana ne bayan jami’i wanda keh shugabantar hukumar lura da cutar sida, kuturta, tarin fuka da cutar cizon sauro (BACATMA) Na bauchi Dakta Sani Mohammed ya bayyana.

A ranar sunyi magana ne dan kimanta cutar tarin fuka wato world tuberculosis day na duniya, wanda akayi jiya litinin. dakta Muhammad yayi magana ne a madadin kwamishin lafiya ta jahar bauchi Dakta Sabiu Gwalabe wanda akayi da manema labarai ya ce ai yawan mutanen sun karu da dubu da dari da hamsin da hudu akan dubu biyar da dari shida da hamsin da hudu wanda aka samu a shekarar dubu biyu da Ashirin da daya.

Hukumar lafiya ta duniya wato world health organization ta saka ranar tarin fuka ta duniya ranan Ashirin da Hudu ga watan Maris na kowace shekara don fadakarwa da ilimantarwa akan cutar tarin fuka ta yanda za ayi a dakileta Kuma akawo karshen wannan annoba ta cutar.

Jahar Bauchi tana da asibitin kula da masu cutar tarin fuka guda dari bakwai da casa’in da hudu (794). Dakta Muhammad Yace gwamnatin Bauchi sun hada kai da wasu manyan hukumomin lafiya don bincike da gano yawan cutar a jahar bauchi.

A cewar sa, ranan tarin fuka ta duniya zata kasance Ana bayani wa mutane a wayar salula, radio da talabijin don karin bayanin yanda za a kiyaye wa cutar. Taimakawa masu cutar da kayan magani da abinci da Kuma gwaji kyauta wa cutar na tarin fuka, sida, ciwon hanta da cutar cizon sauro.

Daraktan hukumar dakile cutar tarin fuka ta bauchi, Yakubu Abdullahi, Yace zasu horar da likitocin yara, da makarantun sakandare da jami’a don gano cutar a jikin yara.

Malam Abdullahi ya qara da cewa gano cutar ta tarin fuka a jikin yara yana da matukar wahala amma sun gano hanya Mai sauki ta gano cutar a cikin bahayar yara.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button