Labaran Yau

Sama Da Mutum 40,000 Ke Mutuwa A Hatsarin Titi Cewar Hukumar Kula Da Hanyar Titi

Sama da mutum 40,000 ke mutuwa a hatsarin titi cewar Hukumar kula da hanyar titi

Hukumar titi ta gwamnatin tarayya Road safety, ta ce sama da mutum dubu 40 ke mutuwa ko wata shekara a dalilin hatsarin mota a Najeriya.

Dauda Biu, jami’in FRSC ya fadi ran litinin a Abuja, a wajen taron Majalisan dinkin duniya na satin kulan titi.

Yace wannan ba shi bane asalin gaskiyar kiyascin yawan mutanen da ke mutuwa ko samun matsala na jiki sanadiyar hatsarin titi.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Ya bayyana cewa mutum miliyan daya da rabi ke mutuwa, Miliyan hamsin kuma ke fuskantar rauni a dalilin hatsarin mota a duniya duk shekara.

A bayanin sa ba wani abun ban tsaro da ya wuce hatsarin titi wa mutane masu shekara 5 zuwa 29. dan a kowani mutuwa hudu na hatsarin titi daya dan wannan shekaru ne masu tafiya da kafa ko a babur ko keke.

“A Najeriya, sama da mutum dubu 40, su ke a mutuwa ta dalilin hatsarin titi” a cewar sa.

Shugaban Hukumar Road safety, yace Majalisan dinkin duniya ta kawo tsari na titin duniya wanda za ayi amfani da ita daga 2021 zuwa 2030.

Biu yace Hukumar ta hada kai da Hukumar lafiya ta duniya WHO da sauran hukumomi masu muhimmanci dan magance hatsarin titi da kiyaye rauni.

An zabi Najeriya dan inganta tukin keke ko babur Kuma Abuja tana da ga cikin jihohi biyar a duniya.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button