Labaran Yau

UNICEF Zatayi Rajistan Haihuwa Wa Yara Miliyan Daya A Bauchi

UNICEF zatayi rajistan haihuwa wa yara miliyan Daya a Bauchi

Kashi 38.3 cikin dari na yara a garin Bauchi aka musu rajistan haihuwa a shekarar 2021.

Dakta Tushar Rane babban jami’in ofishin UNICEF na bauchi, ya bayyana hakan ranar Asabar.

Yace a taron su na kwana biyu sunyi zama na tattunawa kan lamarin, yayinda suka samu rahoton yara kasa da shekara biyar guda miliyan Daya da dubu tamanin da dari tara da tamanin da hudu suke da bukatan rajista a bauchi a shekarar 2023.

Yayi bayani cewa Rajistan haihuwa yana daga cikin muhimman abubuwan da kare yancin yara, dan tsare tsare, girma, da ci gaba da Kuma zama dan kasa.

“Bayan kammala bincike na shekarar 2021, rajistan haihuwa yana kashi 38.3 cikin dari a jihar bauchi.

“A tagwayen aiki da UNICEF da gwamnati tayi, an samu bincike ta Bauchi Tana da cikin masu karancin rajirar haihuwa” a cewar sa.

Mr Mathew Temidayo, daraktan rijistan na Hukumar kidaya ta kasa, yace zasu fara rajistan ne a kananan hukumomi ashirin na jihar bauchi.

Zasu yi aiki da Masu taimako a cikin kauyuka na kowani karamar hukuma wurin rajistan yara kasa da shekara biyar.

Zasuyi aikin tare da Hukumar bautan kasa NYSC, jihar bauchi da kuma gungiyar kananan hukumomi.

Temidayo ya kara da cewa zasuyi rajistan a jihohi ashirin da biyu masu karancin rajistan a fadin kasar.

“Za a fara a watan maris ranar Asirin ga wata, Kuma za ayi sau biyu.
“Kananan hukumomi goma za a fara dasu a cikin kwananki goma sha biyar.Sai a kara yin sauran goman cikin wani kwanan goma sha biyar.

“ Za a nemo masu taimako daga kauyukan dan fito da mutanen da ba a musu rajista ba” ya bayyana.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button