Labaran Yau

Yan Kasuwan Man Fetur Sun Karyata Karin Kudin Mai Zuwa 700

Yan Kasuwan Man Fetur Sun Karyata Karin Kudin Mai Zuwa 700

 

Yan Kasuwan Man Fetur (IPMAN) Sun Karyata Karin farashin Kudin Mai Zuwa naira 700 a kan kowani lita a fadin kasar.

Ciyaman na IPMAN na kudu maso Yamma, Dele Tajudeen, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da akayi dashi ranan jumma’a a Ibadan tare da Hukumar labarai ta kasa.

Shi ciyaman din ya nuna cewa mutane su kori wannan jita jita da razana kan tashin farashin Man fetur.

Ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu Na cire tallafin man fetur, cewar sa dama ya jima da yakamata a cire.

“Inaso in yaba masa wajen cire tallafin kuma Inaso ince Muna goyon baya gabadaya, saboda tallafin man fetur ba komai bane Sai cuta” a cewar sa.

Ya kara da cewa canjin farashin mai da aka samu yazo ne dan tsadan safara na mutane da kaya ne.  Yan Najeriya su kwantar da hankali dan mai zai ishe kowa.

“Inaso inga cewa mutane sun cire jita jitan a zuciyan su, dan Muna kula da lamarin, Kuma babu wani abu kamar kari na farashin

“In zaka kai illorin zai kai dubu 700,000, hakan ya kawo babbancin farashin mai a jihohi.

“Inaso in ce da karfin da ke rataye wuyana da babu gidan Mai da zata siyar da Mai fiye da 515 zuwa 520 a kowani litar.

“NNPC ta bamu farashi daidai da zahiri, Muna siya daga wajen wasu yan kasuwan, saboda ba a NNPCL kawai muke samun mai ba, Muna samu a depon yan kasuwa.

“Duk yanda muka siya man haka Zamu fitar.

“Amma a yau man fetur mai tsada da zaka siya a fadin kasar bai wuce naira 550. Lagos naira 510, jihar Ogun naira 500 da 520”. Tajudeen ya ce.

Kungiyoyin  Sibil society sun yi amanna da cewa barasu yarda da karin farashin Man fetur ba.

Sun bayyana hakan ne a zaman da sukayi da Basil Musa da Haruna maigida suka sanya hanu a madadin kungiyar a Abuja.

Sunyi rantsuwa na rashin yarda da karin man saboda zasu karbe gidajen man yan kasuwa masu zaman kansu IPMAN a kasar.

Sun nuna cewa karin farashin man abunda za a karba bane,

Sun zargi IPMAN da saka mutane cikin kuncin rayuwa. Bayan canxa farashin man fetur babu kallon abinda zai Haifar.

Sibil society sun ce yin hakan karya tattalin arzikin kasa ne, bayan bamu gama fita cikin mamakin cire tallafi da akayi ran 29 ga watan mayu.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button