Labaran Yau

Yuguda Gwamanan Babban Bankin Najeriya

Yuguda Gwamanan Babban Bankin Najeriya

Fata na gari lamiri.Bani taba mancewa, a shekarar 2009, a lokacin Isa Yuguda ya na wa’adin mulkinsa na farko akan kujerar gwamnan jahar Bauchi, al’ummar jahar Bauchi da dama sun yi ta yaɗa jita-jitan wai, Yuguda zai ajiye kujerar gwamnan jahar Bauchi, ya karbi mukamin kujerar gwamnan babban bankin Nigeria (CBN).

Tun daga wannan lokaci har zuwa yau, irin wannan jita-jita na ci gaba da yawo a tsakanin al’ummar jahar Bauchi musamman masoya Malam Isa Yuguda.

Tabbas! Malam Isa Yuguda kwararren maaikancin banki ne wanda babu irin sa a arewa maso gabashin Nigeria. Bayan Yuguda ya kammala digirinsa na farko a fannin tattalin arziki (Economy), yayi aiki a bankuna da dama wanda daga bisani, ya karbi jagorancin jaririyar bankin Inland Bank; banki mallakar gwamnatin jahar Bauchi.

DOWNLOAD ZIP/MP3

A bankin Inland Bank ne Malam Isa Yuguda ya gwada ma duniya irin ƙwazo, hikima da basirar da ubangiji Allah ya azurta shi da shi akan hidimomin gudanar da bankuna da ci gaban tattalin arziki.

A lokacin da Yuguda ya karɓi jagorancin jaririyar bankin Inland Bank, bankin ta na matsayin banki ce mallakar gwamnatin jahar Bauchi, amma a cikin ƙanƙanin lokaci, Yuguda maida ita bankin al’ummar Nigeria baki ɗaya.

Kafin Yuguda ya karɓi jagorancin Inland Bank, bankin ta na da reshe (breach) guda uku ne kacal a jahar Bauchi, amma kafin Yuguda ya bar kan kujerar gagorancin bankin, sai da ya zamanto babu jahar da bankin bata da reshe a Nigeria.

Har zuwa ranar da Yuguda ya bar kan muƙamin kujerar Manajan-daraktan bankin Inland Bank, bubu wata ƙa’ida na kuɗi ko kuma na gudanar da bankuna a Nigeria wanda Babban bakin Nigeria ta gudaya ma bankuna wanda Inland Bank bata cika shi ba.

La’akari da himma, kwazo da azama irin na Malam Isa Yuguda akan hidimomin gudanar da bankuna da ci gaban tattalin arziki, a shekarar 2000, Nal Merchant Bank; babban bankin yan kasuwa a Nigeria ta baima Yuguda mukamin Manajan-darakta.

Babu shakka Malam Isa Yuguda kwararren maaikacin banki ne wanda ba babban bakin Nigeria (CBN) ba, ko mukamin shugaban bankin duniya ka ba shi zai iya rikewa.

Duk da cewa Malam Isa Yuguda bai taba fada mini cewa ya na neman kujerar gwamnan babban bankin Nigeria ba, hakazalika kuma babu wani na kusa da shi da ya taba fada mun haka. Amma kuma, fata na gari lamiri ce, sannan kuma addu’a ce.

Nima na bi sahun al’ummar jahar Bauchi masu addu’ar, ubangiji Allah ya baima Malam Isa Yuguda kujerar shugabancin babban bankin Nigeria. Inda kowa hakan zai kasance, da jahar Bauchi ta tabbata ta haifi da!

Shehu Hassan Makwallah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button