Labaran Yau

Zulum Ya Kara Shekarun Ritaya Da Shekara Biyar Na Malaman..

Zulum ya kara shekarun ritaya da shekara biyar na Malaman Makaranta

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zullum ya kara shekara biyar akan shekarun ritaya na Malaman Makaranta a jihar borno.

An bayyana hakan a takardar da ta zaga daga hukumar koyarwa, wanda permanent secretary, Malam Yusuf Garga ya sanya hannu.

“An janyo hankalin malaman Makaranta kan lamarin, gwamna ya amincewa karin shekaru na aikin malunta daga shekara 35 zuwa 40 na aiki, da Kuma shekara 60 zuwa 65 na malamin, Duk wanda yazo a farko.

“Duk wanda yakeso ya cigaba da aikinsa to Ana bukutan ya rubuta ta hannun shugaban Makarantar da yake da kuma shaidar lafiya daga asibitin gwamnati” yanda tazo cikin takardan.

Malamin ake bukatar ya kai takardar da kanshi in dan nuna sha’awarsa ga aikin.

Shugaba Muhammadu buhari ya rantama hannu kan takardu hudu wanda ciki akwai ta karin shekarun aiki wa malamai a kasar Najeriya a shekarar 2022.

Dailynigeria ta tabbatar da cewa a takardar ta bayyana Sai malami yakai shekara 65 koh kuma yayi aikin shekara 40 Kamin yayi ritayan dole.

Sashi na uku cikin takardar ta bayyana ma’aikacin gwamnati zai yi ritaya in ya kai shekara 60 koh shekarun aiki ta kama shi a 35 amma Banda Malaman Makaranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button