FootballLabaran Yau

Liverpool Sun Daki Bournemouth Kwallo 3 Da 1 A Filin Anfield

Liverpool Sun Daki Bournemouth Kwallo 3 Da 1 A Filin Anfield

Alexis Mac Allister, ya samu jan kati a Anfield bayan minti 13 da dawowa daga hutun rabin lokaci, amma hakan bai hana Liverpool nasara ba.

Liverpool Sun Daki Bournemouth Kwallo 3 Da 1 A Filin Anfield
Liverpool Sun Daki Bournemouth Kwallo 3 Da 1 A Filin Anfield

Liverpool sun tsorata daga farko, saboda kwallon da “Antonie Semenyo” ya musu sammako a minti 3 na farkon lokaci, kwallon ta dawo wa Semenyo ne bayan “Andy Robertson” ya tare harin da “Dominic Solanke” yayi kokarin kaiwa,
Semenyo ya buga kwallon da karfi wadda yasa golan Liverpool ya kafe.

A minti biyu na farkon rabin lokaci “Jaidon Anthony, ya jefa kwallo a ragar Liverpool a dalilin rudanin da aka samu tsakanin masu tsaron gida da gola wadda matemakin alkalin wasa na kan layi ya daga offside bayan Bournemouth sun gama murna.

Golan Liverpool “Alisson” ya samu yelon kati a minti 8 na farkon rabin lokaci, dalilin ya kwashe dan wasan Bournemouth “Anthony” a gaban raga a waje, saboda yayi yunkurin sace kwallon da golan yayi ganganci dashi.

Bayan hare-hare masu yawa da Liverpool suka kai a rabin lokaci na farko, “Diogo Jota” yayi nasarar bawa “Luis Diaz” kwallo a gaban ragan Bournemouth inda yayi karamin watsewa da kwallo zuwa cikin ragan nasu a minti 27, wannan cin ya karawa mabiya bayan Liverpool karfin gwiwa da kuma sauran yan wasan.

Liverpool Sun Daki Bournemouth Kwallo 3 Da 1 A Filin Anfield
Liverpool Sun Daki Bournemouth Kwallo 3 Da 1 A Filin Anfield

Liverpool sun samu “bugun kai tsaye da gola”(penalty) a minti 35,”. Joe Rothwell” ne yasa kafa wa “Dominik Szoboszlai” a gaban raga yayin kare gida. “Mohamed salah” ne ya hau bugun kai tsaye wa Liverpool inda Golan Bournemouth “Neto” ya tare harin farko a hanun dama, Salah ya sake maida ita ta hanun hagu inda golan babu yadda ya iya haka kwallon ta shiga raga.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, “Alexis Mac Allister” yakai kafa wa kwallo inda yasa wa “Ryan Christie” tokari a gaban ragar Bournemouth, har alkalin wasa ya bashi jan kati.

Liverpool basu karaya ba bayan yan wasan su sun dawo goma a cikin fili.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button