Gabriel Iliya Magaji, mai shekaru 38, mazaunin Masaka da ke karamar hukumar Karu ta Jihar Nasarawa, ya kashe kansa ne bayan ya samu labarin cewa matarsa na yin zina da abokansa domin neman kudi.
A safiyar ranar Litinin aka tsinci gawar Magaji a cikin azuzuwan makarantar Crystal da ke Masaka.
A cewar DSP Nansel Ramhan, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, an tabbatar da faruwar lamarin.
Jami’an ‘yan sanda sun amshi rahoton inda suka kai gawar zuwa babban asibitin inda aka tabbatar da cewa mutumin ya mutu.
Sai dai mai magana da yawun ‘yan sandan ya bayyana cewa, ya kasa tantance ko mutumin ya kashe kansa ne sakamakon wasu abokansa da suka yi lalata da matarsa.
Ana ci gaba da bincike duk da cewa ba a gano takardar kashe kansa ba.
A cewar wani wanda ke da masaniya a kan lamarin, yace Magaji ya kashe kansa ne bayan ya fuskanci abokiyar aurensa.
Wanda a cewarta ta kasance mai gaskiya a kan zinar da suka yi, kuma harda yin ikirarin cewa tayi yi amfani da kudin ne wajen biyan bukatun iyalinsu musamman na yaransu.
Dan Alheri, a nasa bangaren, ya bayyana cewa mutumin ya bata rai ne bayan da ya samu labarin cewa abokansa suna kokarin saduwa da matarsa.