Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain (PSG) ta ki biyan bashin Kylian Mbappe kusan fam miliyan £50 a matsayin albashi mai tsoka duk da cewa an tilasta mata yin hakan.
Hukumar LFP, mai kula da harkokin kwallon kafa ta Faransa, ta umurci zakarun gasar Faransa ta League 1 da su biya Mbappe kudaden shi na tallafi da albashin da ba a biya ba daga zamansa na tsawon shekaru bakwai a birnin Paris, amma sun bayyana cewa ba za su biya ba.
Ana kyautata zaton Mbappe ya tuntubi UEFA a watan da ya gabata kan rashin jituwar albashi.
A sanarwar kungiyar ta ce kamar haka:
“Idan akayi la’akari da iyakokin doka na kwamitin don yanke hukunci game da wannan shari’ar, yanzu dole ne a garzaya da shari’ar a gaban wani hukumci, wanda PSG za ta yi farin cikin gabatar da duk gaskiyar a cikin watanni da shekaru masu zuwa.“
P.S.G dai ta ji takaicin Mbappé bayan tayi masa tayin mafi tsada a tarihin kungiyar, wadda ya kulla a shekarar 2022. Sai dai Mbappé bai gamsu ba saboda yana ganin an karya alkawarin da ya dauka na sayen manyan ‘yan wasa.