“Cristiano Ronaldo Besan Me Yake Fada Ba” – Erik Ten Hag
Erik-ten Hag ya mayarwa da Cristiano Ronaldo martani, yana mai cewa dan wasan gaban Portugal din bai san me yake magana akai ba saboda ya yi nisa da Manchester”.
Ronaldo ya soki Ten Hag a wani faifan bidiyo da Rio Ferdinand ya shirya, yana mai cewa bai kamata kocin United ya ce “ba za su yi fadan lashe gasar cin kofin zakarun Turai ko Champions League ba.”
A daya bangaren, Ten Hag, ya musanta kalaman, inda ya ce Ronaldo ne ya bayyana cewa United ba za ta iya lashe gasar Premier League ba.
“Ya fadi cewa; Manchester United ba za ta iya lashe gasar Premier ba,“ in ji Ten Hag, wanda ya yi rashin jituwa da Ronaldo a lokacin da suke tare a kulob din.
“Ya fadi haka, idan kun karanta labarin sosai, yana da nisa a Saudiyya, nesa da Manchester don kowa ya sami ra’ayi kuma yana da hakkin ya sami ra’ayi. Babu kyau.”