Labaran Yau

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Magance Matsalan Tattalin Arzikin Nigeria

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Magance Matsalan Tattalin Arzikin Nigeria

Ayayin da tsarukan shugaba Tinubu suna kama da na kwarai da zasu bada sakamako mai kyau, duk da haka wannan tsaruka da bai kamata su saba doka ba kuma bai dace sun jefa `yan kasa cikin talauci ba.

Har yanzu bai cika wata daya da rantsar da shugaban kasar Nigeria Ahmed Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, shugaban ya kawo gyare gyare da tsaruka ga tattalin arzikin kasar nan wasu daga ciki tsaruka ne na shawarwari da masana tattalin arzikin sukayi kai har ma da hukumomi na harkar tattalin arziki a duniya baki daya.

Shugaba Tinubu ya samu tattalin arzikin kasar Nigeria da matsaltsalu masu dumbin yawa, wanda tattalin arzikin na 2022 da ya karu akan na baya da kashi 3.1% da watanni ukun farko na shekarar. farfadowar da yayi daga Cutar Corona wadda ta haddasa fadawa yanayi na rashin dadi kama daga fannin kasuwanci na saye da sayarwa da yake tafiyar hawainiya.

DOWNLOAD HERE

Saye da sayarwar kasar dai yana da adadi na dala biliyan $2.85b wanda ya ci baya sosai idan aka hada shi da na 2014 wanda yake da adadin dala ta amurka biliyan $54.1b.

Sannan kuma kudaden da kasashen waje suka saka a Nigeria din ya sauko daga dalar Amurka $2.2b a shekarar 2014 izuwa Dalar Amurka miliyan $0.47m. Matsalolin kasafin kudi ya samu karin kashi 370.54% daga shekarar 2016 zuwa 2023, sannan kuma kudaden bashi da ake biya da kasar ta ciwo a baya ya fi adadin kudin da kasar ke samar wa kanta sau goma cikin shekaru goma na baya.

Adadin basussukan da ake bin Nigeria a watan Yuni na 2013 shine Naira tiriliyan N7.93tr. wanda kuma a yanzu ya kai adadin Naira Tiriliyan N77tr.

DOWNLOAD MP3 HERE

Cikin wanna lokacin basussukan waje na kasar ya karu ne da kashi 473% ayin da basussukan na ciki ya karu da kashi 7029%. Basussukan da Babban bankin kasar CBN ta bawa kasar wadanda masana ke cewa ba na tsari baneya taimaka wajen jefa kasar cikin karin tsadar ababen masarufi da more rayuwa akan adadin 22.41% a cikin wata Mayu na shekarar da muke ciki.

Wadannan ababe na hade da matsalar rashin tsaro da kasar ke fuskanta ya bada gudunmawa wajen tashin kudin abinci, yayin da kashi 63% na kasar ke rayuwa cikin matsanancin talauci. Matsalar rashin aikin yi na da kashi 33.3% a shekarar 2022, KPMG sun lissafa ya haura sama da kashi 40.6% cikin shekarar 2023.

A yayin wata ganawa da Shugaban kasar yayi da mutane yayin da yake yakin neman zaben sa shugaban yayi alkawarin kawo gyara ga bangarori na matsaltsalun kasar mafi girma guda biyu wanda sune tsayar da kasafin Man fetur da gwamnatin ke biya da kuma kawo dauki ga kudin kasar me faduwa warwas lokaci zuwa lokaci.

An shawarci shugaban Nigeria Ahmed Tinubu da ya tuna da talaka a duk irin tsarukan da zai kawo saboda wahalar da talakan kasar ke sha na da matukar yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button