Sama Da Layukan Wayoyi Miliyan 73 Sun Shiga Gara- Hukumar NIMC
Fiye da layukan waya a Nijeriya sama da miliyan 73 na cikin garari sakamakon dakatar da su daga kiran waya saboda kin hada su da lambar dan kasa (NIN).
Datse layukan ya faru ne sakamakon umarnin da gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanonin sadarwa, na cewa duk layin da ba a hada shi da lambar dan kasa ba, to a rufe shi sakamakon wa’adin da aka dauka ya cika.
Wannan umurni yana kunshe a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa wanda jami’in hulda da jama’a na hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa (NCC), Dakta Ikechukwu Adinde da shugaban hukumar kula da katin dan kasa (NIMC), Kayode Olagoke suka fitar. Sun bayyana cewa umurnin ya fara aiki ne tun a ranar Litinin, 4 ga watan Afrilu ya fara aiki.