Labaran Yau

Majalisan Dattawa Ta Tabbatar Da Nadin Hafsoshin Tsaro Na….

Majalisan Dattawa Ta Tabbatar Da Nadin Hafsoshin Tsaro Na kasa

Majalisan dattawa ta tantance sabbin hafsoshin tsaro na kasa wanda shugaban kasa Tinubu ya nada.

Wanda aka tabbatar sun hada da Major Janar Christopher Musa, a matsayin shugaban tsaro na kasa. Major Janar Taoreed Lagbaja a matsayin shugaban sojin kasa.

Cikin wanda aka tabbatar harda Rear Admiral Emmanuel Ogalla a matsayin Shugaban sojin ruwa. Air Vice Marshal Hassan Abubakar a matsayin shugaban sojin sama.

DOWNLOAD MP3

Shugaban Majalisan dattawa Godswil Akpabio, yace Jan daki ta karbi neman amincewar hafsoshin tsaro na kasa Kuma ta tabbatar dasu a matsayin hafsoshin tsaro na kasa.

Yace hafsoshin tsaron sun amsa tambayoyi wajen yan Majalisan dattawa kan tsaro da Kuma yanda zasu kawo sauyi kan tsaron kasa.

DOWNLOAD ZIP

Hafsoshin tsaron kowani mutum daya an bashi minti daya domin gabatarda kansu. Kamin tantancewar ya koma bayan kofa saboda tsaro na kasa.

Majalisan dattawa ta daga kafa kan wasu dokokinsu yayin da Mai bawa shugaban kasa shawara kan Majalisan tarayya, Sanata Abdullahi Gumel ya shigo da hafsoshin tsaron Majalisan dattawa.

A takardan da shugaban Majalisan dattawa Godswil Akpabio ranar talata a satin da ta gabata, Tinubu ya nemi su tabbatar da zaben Hafsoshin tsaro na kasa.

Tinubu yace neman tabbatar war yazo da dokar kirkiran Sojin kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button