Labaran Yau

Rikici Tsakanin PSG Da Mbappe Na Kara Tsamari

Rikici Tsakanin PSG Da Mbappe Na Kara Tsamari

Rikici Tsakanin PSG Da Mbappe Na Kara Tsamari
Rikici Tsakanin PSG Da Mbappe Na Kara Tsamari

Rikici tsakanin Kungiyar kwallon kafa dake kasar faransa wato Paris sait Germain da Dan wasan kasar faransa wato kylian mbappe na daukan sabon salo.

A jiya ne kungiyar ta fitar da sunayen yan wasan da zasu shiga atisayen da kungiyar zatayi inda aka cire sunan Dan wasan. Wannan ya biyo bayan zargin da mai kungiyar wato al khaleifi yayi na cewa mbappe yana ganawar sirri da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid inda har yake zargin sun cimma yarjejeniya na kudin da zai dinga dauka.
A baya bayan nan daraktan wasanni na kungiyar yayi ganawa da manema labarai inda yake cewa kungiyoyi da yawa sun ci gasar zakarun nahiyar turai ba tare da mbappe ba dan haka suma zasu cigaba da wasannin su ko babu Dan wasan.

Rikici Tsakanin PSG Da Mbappe Na Kara Tsamari
Rikici Tsakanin PSG Da Mbappe Na Kara Tsamari

Kungiyar ta bawa Dan wasan daga yanzu zuwa 31 ga watan yuli domin ya sabunta kwantaraginsa ko kuma su siyar dashi zuwa kungiyar kwallon kafa ta Al hilal dake Saudi Arabia. Ana zargin Dan wasan yanaso ya karasa kwantaraginsa ne sai ya tafi Real Madrid kyauta a kakar wasanni mai zuwa.

DOWNLOAD MP3

Rahotanni sun nuna cewa akwai kungiyoyi guda biyu a kasar ingila da suka nuna sha’awar daukan Dan wasan mai shekaru ashirin da hudu Wanda suka hada da Chelsea da wata kungiyar da baa fadi sunanta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button