Ko Yesu Zai Iya Yaudara Osibanjo Mayaudari Ne- Kungiyar Kiristocin Arewa
Kungiyar Kiristocin Arewa watau Northern Christians Movement (NCM) ta gargadi yan siyasa da Malamai su yi hattara da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Kungiyar tace ta yi hasashen cewa Osinbajo mutum ne wanda zai yaudari duk wanda ya taimakesa.
Wannan ya biyo bayan ayyana niyyar takarar kujerar shugaban kasa da Farfesa Yemi Osinbajo yayi ranar Litinin din data Gabata.
Osinbajo wanda ke ikirarin shi Fasto ne na cocin RCCG, yayi watsi da irin alakar da ya gudana tsakanin Apotle Paul da yaron gidansa Timothy, saboda ya bi haka wajen alakar tsakaninsa da maigidansa, Asiwaju Bola TInubu.” “Osinbajo ya yaudari Tinubu kuma ya watsa masa kasa a ido ta hanyar neman kujerar da yake nema.
Rabaran Jonah ya kara da kawai Osinbajo ya dogara ne da kuri’un mambobin cocinsa milyan 12 amma yana gargadin mammalakin cocin RCCG cewa idan ya goyi bayan Osinbajo, shima a kwana a tashi sai ya yaudare sa. Yace: “Kamar yadda ake cikin makon da Judas ya yaudari Yesu, haka Yemi Osinbajo zai yaudaru Adeboye yadda ya yaudari Tinubu, saboda halina kenan.