Labaran Yau

An Dakatar Da Messi Daga Buga Kwallo Na Sati Biyu Dan Tafiyar Sa…

An dakatar da Messi daga buga kwallo na sati biyu dan tafiyar sa Saudi Arabia

Dan kwallon Gaba na wasan PSG Lionel Messi, ya samu dakatar war buga kwallo na sati biyu bayan tafiyar da yayi babu masaniya zuwa saudiyya.

Dan wasan kwallon Argentinan an haramta mai buga kwallo koh da na motsa jiki ne, Kuma za rage kudin Albashin sa cikin wannan lokacin haramcin. Manema labari suka bayyana hakan ranan talata.

Messi bare samu halin buga wasan da za ayi ba na league 1 wanda zasu kara da Troyes da Ajaccio, amma zai dawo ya buga da Auxerre ran 21 ga watan mayu.

DOWNLOAD MP3

A jadawalin, Ta nuna PSG tafi kowa maki, wanda ya samu maki 75 a cikin wasanni 33.
Daily Nigeria ta rawaito.

A shafin yanan gizo mutane sun fito sunyi korafin cewa PSG bata da hurumin hana shi zuwa inda yakeso yaje.

Wasu Kuma sun bayyana cewa Suna tsoron kar a siye shi ne a kasar saudiyya tunda kowa ya fahimci irin arzikin da suke dashi wajen siya da biyan dan kwallo.

DOWNLOAD ZIP

A inda aka ji tsoron kar a siyeshi kamar yadda Alnasr ta siye Christiano Ronaldo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button