Waye Dan Social Media – Lukman MD Baba
WAYE DAN SOCIAL MEDIA 001
Wannan batu ne na gaskiya amma fa akwai ɗaci… Dan Social Media shine wanda yake taimakawa wajen fito da duk wani mai bukatar siyasa, ya kuma tallata shi da kudinshi
Bincike ya tabbatar da akalla duk dan Social Media yana kashe sama da Dubu Dari a shekara wajen temakawa wanda yake Kauna.
WAYAR HANNUNSHI N30,000.00
DATA N200 KULLUN = WATA N6,000 SHEKARA N72,000
7,2000+30,000 = N102,000. A TENURE DAYA 4YEARS N408,000.
INDA MATSALAR TAKE ITACE.
1. A duk Shekara Dan Media sau daya ake tunawa dashi, azumi ko sallah.
2. Babu wani jagoran Siyasa dayake siyawa yan media Waya.
3. Idan ankafa Gwamnati babban abunda zai rabauta dashi bai wuce injin markade ba ko yan tsaki, sun mutu kafin yaje gida.
4. Idan anyi Mutuwa kuwa Dan Media ake fara nema ya sanar.
5. Da wuya kaga dan gidan wanda ake yadawa yana like ko comments ballantana ya miko sako.amma idan an samu gwamnatin da shi za afara wato shi zai tafi scholarship.
6. Duk karfin ka a Media baza a biya maka kudin makaranta ba, balle jari.
7. Duk gogewarka da iya kwalliya ubangidanka bazai yadda ka auri yarshi ba, domin Dan jagaliya yake kallonka kamar yadda wadanda suka ci moriyar karatun Gwamnatin Jiha suke kallon yan media.
8. Sannan idan kana tare dasu sai kaji suna cewa bata lokacine Facebook.
MAFITA ITACE:
Ka san kanka katashi ka nemi naka.
Kasan da wa kake tare kuma ya mutuncin ka yake agunshi.
Kada ka yarda da ankarbo daga wane shima yakarbo daga wancan, a kaika gindin maganin a sanka.
Dan Social Media tamkar rodi yake a siyasar kasar nan idan ba’a kafa da shi ba to ginin bazai yuba.
Saboda haka ina kira ga abokaina yan media damu San abinyi tun kafin muyi danasanin tallata mutanen daba mune a gabansu ba.