Labaran Yau

Yadda Na Canza Sakamakon Jarabawa Ta Jamb, Mmesoma Ta bayyana

Yadda Na Canza Sakamakon Jarabawa Ta Jamb, Mmesoma Ta bayyana

Ejikeme Mmesoma, Yar shekara 19, dalibar Makarantar Anglican Girls wanda ke garin Uruagu Nnewi na jihar Anambra. Ya bayyana yanda ta canza sakamakon jarabawan ta.

Mmesoma ta bazu a kafafen labarai tun bayan Hukumar jarabawa ta Jamb ta bayyana cewa ba ita tafi kowa cin Jarabawar ba, A jarabawan da aka rubuta ta jamb na shekarar 2023.

Jamb tace yarinyar taci 249 a jarabawan ba 362 ba wanda ita ta ke bayyana wa, amma ita dalibar tayi bidiyo inda take nuna cewa lallai ga abinda ya ci.

Hakan ya kawo sabanin tunani a kasa gaba daya, har ya kai da Gwamna Charles Soludo na Anambra ya saka kwamitin bincike akan lamarin.

Amma kwanaki kadan cikin bincike wanda mutum takwas keyi, Mmesoma ta karayin bidiyo ta karyata kanta cewa ba haka sakamakon ta yake ba na cin 362.

A rahoton, kwamitin ta saka dalibar ta bada hakuri wa Hukumar jarabawa ta jamb.

A cikin rahoton kwamitin, An gayyace mmesoma da Ma’aikatan Hukumar Jamb da Kuma malaman Makarantar da tayi.

“Ejikeme Joy Mmesoma, ta bayyana cewa ta canza sakamakon jarabawan ta da kanta wajen amfani da wayan ta.

“Ta amince da laifin a gaban Principal na Makarantar su, Sakataren Ilimi cewa abinda Jamb ta fada Gaskiya ne, akan abinda ya faru. Ya bayyana bada sakamakon da ba daidai ba da kanta babu taimakon kowa da Kuma amfani da lamar waya mai layin Airtel.

“Principal na Anglican Girls Sakandare Mrs Edu Uche, ta nuna rashin jindadi kan lamarin gaba daya.

“A bayanin ta taje kafe na Prisca Global computers, Uruagu a garin Nnewi ta printing sakamakon da ta canza. Da wannan lamarta na Airtel” Rahoton ta bayyana.

Rahoton ta bayyana cewa dalibar Tana sane da asalin makin da ta ci na jarabawan, tayi iya kokarin ta dan ta canza.

“Sakamakon jarabawan mai dauke da suna Ejikeme Joy Mmesoma da maki 362 Mai dauke da  adireshin jarabawa, ranan haihuwa da sauransu ba sahihiya bace, sakamakon bogi ne.

“Ma’aikatan Hukumar Jarabawa ta Jamb, wanda ya jagoranci tafiyar Dakta Fabian Benjamin ya bayyana yadda abun ya faru, da Kuma yadda ita Mmseoma Joy da lambar rajista 20230639047FF tayi wajen canza sakamakon ta.

“Hukumar Jamb ta nuna cewa dalibar da saninta ta tura wa jamb da lambar ta yadda takeson makinta ya fito, yayin da ta rubuta lamar rajistan ta tare da subject da maki, Eng:98, Phy: 89, Bio 94, da Chem: 81, bayan nan Sai Jamb ta tura mata da abinda ta samu 249”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button