KannywoodLabaran Yau

SHAWARA: Idan Kukaje Ku Biyu Ai Zakufi Yin Hirar Arziki Kuma Zaku Natsu – Jamila Ibrahim

Duk mace Mai Tara kawaye ba kalar aure bace

Yauma shahararriyar jarumar kafar Fezbuk tayi tsokaci kan yanda mata ke tara kawaye bayan sunyi aure.

Jami’inmu na Labaranyau Blog baya gajiyawa wajen kawo muku shawarin Jamila Ibrahim wanda a baya tayi magana akan Jike jike da mata da maza ke sha wanda ke janyo matsaloli wajen zaman takewar aure.

DOWNLOAD MP3

Yau dai ta sake juyowa takan mata yanda suke kuskuren tara kawaye

Mundin kaga yarinya budurwa da dandazon kawaye Lodi Lodi inda Hali ka rabu da ita , kaga waenan she*gun kawayen dayawa Basu kulla Alkhairi sai tsiya , kullun so suke kawarsu tayi aure ta dinga Basu labarin zamantakewar ku..

In ma soyayya kuke kawayen sune committee na zugi da za*gin saurayi…

DOWNLOAD ZIP

Yo banda Hali irinta tsi*ya sabida meh saurayi zaice kizo in kaiki kici abinci sannan ki gayyato kawayenki ba tareda kin sanar dashi ba sannan har kuci abinci na dubu Dari biyu da ashirin kice ya biya 🤔🤔🤔

Ai gayen ya biyani da ya gudu Bai biya ba

Banda rashin lissafi idan kukaje ku biyu ai zakufi yin hirar arziki kuma zaku natsu ku fahimci juna , chanji zai rage har a Baki na kashewa a ciki..

Amma dan Rashin lissafi wasu mata sun dauka burgewa ne ace za’a kaiki cin abinci ki gayyato kawaye 😴

Ai ni bazan ma iya Kai wata kawata inda saurayina yake ba , gudun kar ta ganshi kyakyawa ta kwacemin shi 😄😄😄

Har in gama soyayya mu rabu babu mai sanin kalar saurayi na ko a hoto 🤣

Meh zakace dangane da shawarin Jamila Ibrahim?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button