Gwamnatin Kaduna ta kafa dokan hana fita a sabon garin Nasarawa
A jiya Litinin Gwamnatin jihar kaduna ta kafa dokan zaman gida a Sabon garin Nasarawa layin Tirkaniya na karamar hukumar chikun.
Kwamishinan tsaro da gudanarwar cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce in dau wannan matakin ne dan ayi duba da abinda keh jawo a karya doka da oda.
Yace,
“ An yanke shawaran ne bayan karya doka da oda da akayi wanda jawo tashin hankali yakai da rasa rayukan mutum biyu a hargitsin yan dana.
“ Jami’an tsaro sun karbi odan Domin tabbatar da dokan zaman gida na wannan yanki don yin bincike akan lamarin.
Suna kira da mutane su bi dokan zaman gidan a wannan yankin, wanda an farashi tun jiya litinin.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa zasu bayyana duk abinda keh tafe yanda yakamata.