Labaran Yau

Rukunnan Gwamnati 3 Zasu Raba Naira Tiriliyan 1.7 Don Amfani A…

Rukunnan Gwamnati 3 Zasu Raba Naira Tiriliyan 1.7 Don Amfani A Watan Yuli

Rukunnai uku na gwamnati na Shirin raba kudaden sun a watan Yuli. Rukunnan gwamnatin wanda sune Gwamnatin tarayya, na Jihohi, da Kananan hukumomi za su raba Naira Tiriliyan 1.959 a watan Yuli 2023.

Tsarin da doka ta bayar ya kunshi Naira tiriliyan 1.7 na kudaden shiga da gwamnatin tarayya ta tara, sai kuma Naira biliyan 293 daga VAT, da kuma Naira biliyan 12 daga kudaden shiga na harajin kudade da aka tura su ta yanar gizo.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin mai magana da yawun sakataren gwamnatin tarayya a jiya yayin da yake ganawa da manema labarai a Ofishin sa jiya. inda ya bayyana cewa kudaden sun hadar da kudin da gwamnatin tarayya ke turawa jahohi domin a biya albashin ma`aikata sa`annan kananan hukumomi su biya nasu albashin da kuma kudaden aiki na ma`aikatun su da duk wani abu da ya shafi aiki a bangarorin uku.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button