Labaran Yau

Anci Mutunci, An Kama Peter Obi A London Cewar Mambobin..

Anci Mutunci, an kama Peter Obi a london cewar mambobin campaign dinsa

Ofishin shugaban yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar ya fada akan dan takarar jam’iyyar wato Peter obi yasha cin mutunci tsaff a wajen jami’an iyaka na babban birnin amurka a wani tashan Jirgin sama (heathrow) dake London.

Wanda yayi magana a madadin kungiyar yakin neman zaben, Diran onifade, a maganar da yayi ranar laraba yace tsohon gwamnan anambran yasha tambayoyin da dakatarwar bisa lefin da ake magana akan wani na basaja akan shine Peter Obi din.

Ya fada akan Obi, wanda dawowanshi Kenan daga london inda yaje yayi shagalin bikin easter, ya samu ya kubuta ne saboda daukin da yan najeriya suka kawo mai a tashan jirgin saman (heathrow) dake london.

Onifade ya bayyana cewa dan takarar LP ya sauka a filin jirgin Heathrow a london daga Najeriya ran jumma’ah, bakwai ga watan Aprailu a shekarar 2023.

Yayin da obi yake kokarin shiga layin tantaancewa, jami’an immigration suka bashi takardar kame kuma aka fadamishi cewa ya koma gefe.

An mai tambayoyi dayawa kuma abin ya kasance abun mamaki ma Wanda ya zauna fiye da shekara goma a wajen.

Tunda fuskar Obi sananne ne a idon yan Najeriya gida da waje, Sai yasa mutane suka daga hankali dan jimawa da yayi a hanun hukuma.

Jami’an fita da shiga suma an tilastasu su fadi wanda suke wajen da sukayi wa Obi tambayoyi inji cewar Onifade.

Ya kara da cewa wani keh shigar Obi yana abubuwa wanda bashi kan ka’ida wanda zai batawa dan takarar suna.

A halin yanzu meh shigar Obi har izuwa yanzu ba ganshi ba.

Hakan zaisa a daure Obi akan abinda beh aikata ba, Kuma zaiyi amfani da hakan wajen tozarta dan takarar da iyalensa, da jam’iyarsa, da kuma masu goyon bayansa.

Ya bayyana cewa Peter Obi ya fuskanci barazana tun Kamin zaben da ta gabata ran 25 ga watan biyu wanda yazo na uku a sakamakon zaben wanda hukumar zabe ta bayyana.

Tunda ya fadi zabe yanada yancin zuwa kotu idan yanaso tunda yan kasashen waje sun tabbatar cewa zaben akwai badakala da rashin Gaskiya ciki.

Onifade ya kara da cewa gwamnatin tarayya sun cewa dan takarar yaje kotu, amma kuma an tura Ministan zantarwa yaje Amurka dan ya bata dan takarar nasu da cin amanan kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button