Ortom ya janya kararsa ya rungumi kaddaran zabe
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya janye kararsa da yayi a kotu akan Dr Titus Zam, na jam’iyar APC Da kuma hukumar zabe akan batunsa na sakamakon zabe da ya daukaka kara.
Shi sabon sanatan jihar benue ta Arewa maso yamma ya lashe zaben da kuri’a 143,151 Wanda ya doke gwamnan jihar Meh ci Samuel ortom da kuri’a 106,882 a zaben sanata da akayi a watan fabrairu Ashirin da biyar ga wata lokacin zaben shugaban kasa dana sanatoci da majalisan tarayya.
Shi gwamna Ortom ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da mambobinsu na PDP da kuma wanda suka tayashi wajen gwagwarmayan neman kujerar sanata a yau talata 28 ga watan maris.
Yace ya janye karar ne domin gudun badakalar zabe, Duk da dai a cewarsa yanada hujjojinsa wanda zai iya bayyanawa akan badakaloli da akayi a zaben da ya gabata. Saboda sakamakon zaben wasu ba sakasu a shafin yanar gizo na INEC ba.
Ya kara da jadadda cewa ya yanke shawaran janye karar ne dan samuwar zaman lafiya a jam’Iyar su bayan wasu yan jam’Iyar sun daukaka kara.
Ortom ya tabbatar da cewa zai cigaba da aiki tuquru dan samun cigaba wa jihar a ta kowani fanni na cigaba.
Ya kara da yabawa jama’an jihar benue wajen jajircewansu suka fito suka kada zabe a halin bacin rai da gwamnatin tarayya ta basu.
Mista Samuel ya bayyana godiyan sa wa jam’Iyar PDP da goyon bayan da suka bashi na zama gwamnan jihar benue da Kuma a matsayin sa na gwamna. Kuma yace ya yafewa Duk wanda yayiwa ba daidai ba kuma yana neman gafaran duk wanda bata musu.
Yana Kuma Meh miqa godiyarsa wa ubangiji da ya bashi damar yin mulki a jihar benue wanda yake kyautata zaton yayi adalci a matsayin sa na gwamna. Labari daga dailyNigeria.