Labaran YauPolitics

Binciken Jam’iyar APC Na Jahar Gombe Kan Zagon Kasan Da Akayi Zaben Daya Gabata

Jam’iyar APC na Jihar Gombe tayi bincike kan Sanata da dan majalisan tarayya akan zagon kasa da sukayi a zaben da ta gabata.

A jiya talata Manema labarai suka tattauna da Samaila Ali wanda ya kasance sakatare na jam’Iyar APC ta Lubo/Difa/kinafa ward ta kamar hukumar Yamaltu Deba a jihar gombe.

A fadin sa Suna zargin dan majalisan tarayya Yunusa Abubakar da hadin kai wajen cin amanan jam’iya da hada kai da jam’iyar abokan takara a zaben gwamnoni da yan majalisu da ta gabata.

A cewar sa dan majalisan tarayya ya umurci yan jam’Iyar da su zabi wani jam’Iyar ba APC ba.

DOWNLOAD MP3

Haka, shugaban APC ta ward din bambam na karamar hukumar Balanga sun hada kwamiti na mutum biyar don bincike kan sanatan Gombe ta kudu, Amos Bulus da yin zagon kasa wa Jam’Iyar APC a lokacin zabe.

Ya kara da bayyana cewa shi sanatan yaki kasance wa tare dasu tun daga lokacin campaign Kuma ya fadawa magoya bayansa dasu zabi wata jam’iya ta daban a lokacin zabe.

Ita jam’iyar APC ta jihar Gombe barata lamunta ba dan sanata da dan majalisan tarayya Masu ci da wasu mambobin jam’Iyar akan cin Amana da butulci ba, Kuma jam’iya a shirye take don daukar matakin da yakamata.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button