Zan bar kasar da cigaba fiye da yadda muka samu a 2015- Buhari
Shugaban kasa Muhammadu buhari, Yace zai bar ofishi da tabbacin barin kasar cikin cigaba fiye da yadda ya tarar a shekarar 2015.
Shugaban kasan ya bayyana hakan a jawabin sa na barin ofishi ranan lahadi a Abuja.
Buhari ya bayyana jindadi ga wanda suka taimaka da goyon baya dan tafiyar cigaban Najeriya.
“Zanyi amfani da wannan dama dan nuna godiya wa duk yan Najeriya da suka bada gudumawa da goyon baya dan cin ma nasaran tafiyar kawo cigaba a kasar.
“Baran iya manta wa da miliyoyin yan Najeriya da suka Mun addua lokacin da na fadi rashin lafiya tenure ta na farko ba, Ina muku addua da zaman lafiyar kasa gaba daya.
“Yayin da nayi ritaya zuwa daura, jihar katsina.
Ina mai cike da samun nutsuwa dan Mun dau hanyan kawo sabuwar kasa Najeriya. Kuma gwamnati mai shigowa zatayi abinda ya dace dan Gina kasar” in ji shi
Hukumar labarai ta kasa ta bada rahoton cewa shugaban kasa Mai barin gado yayi amfani da jawabi wa kasan wajen cigaban da ya kawo wa kasa a shekara takwas da ta gabata.
Akan mu’amalar kasa da kasa, buhari Yace da girma da samun karamci inda ta samu shugabancin manya manyan hukumomin duniya.
Ya yabawa samun hadin kan yan majalisa da ya samu, da Kuma nuna godiyan sa wa shugabancin Majalisan tarayyan da goyon bayan da ya samu.
Ya ce, “ Tsarin shugabancin an gina ta ne da cigaba da rabe raben karfi na mulki.
Akan tsaro, buhari yace gwamnatin shi tayi kokari wajen rage yan ta’adda, yan bindiga, yan fashi da Kuma wasu laifuffuka.
“Yakin mu a Najeriya dan mu samawa yan Najeriya wurin zama da tsaro, Kuma ancin ma nasara.
“Yayin da na kammala aiki na, mun yi kokari rage ta’addanci, kashe kashe da sace sace da sauran laifukan” ya ce.
Shugaban kasan yana kira wa yan Najeriya da su bawa jami’an tsaro goyon baya da hadin kai dan kau da matsalar ta’addanci.”kasa ta na samun kima ne in mutane sun zama yan uwan juna”.
Buhari ya bayyana rashin jindadinsa kan wanda suke hannun yan garkuwa, yace kuma jami’an tsaro suna aiki dan sake su cikin koshin lafiya.
Akan yaki da rashawa a shekara takwas da ta gabata, buhari Yace “ kun san yadda zuciya ta take dan kau da rashawa a kasar, wanda ta dukufar da gudanarwar gwamnatin da kawo cigaba.
“Nayi yakin matuka Duk da kalubalen da aka fuskanta bai sa Mun rusuna ba.
“Ina jindadi dan mun karbo kudade da yawa sun dawo kasa Najeriya Kuma Mun karbe gine ginen da aka siya da dukiyar kasa”.
Daily Nigeria ta rawaito