Labaran Yau

Buhari Ya Sanya Hanu Kan Dokar Almajiranci Da Yaran Da Basu Zuwa Makaranta

Buhari ya sanya hanu kan Dokar Almajiranci da yaran da basu zuwa Makaranta

Shugaban kasa Muhammadu buhari Ya sanya hanu dan amincewa bude Hukumar kula da Almajiranci da yaran da basu zuwa Makaranta dan kau da kalubale da suke fuskanta.

Dokar da ta samu goyon bayan Balarabe Shehu kakale da wasu mutum sha takwas, dan Samar da Hukumar Almajiranci da yaran da basu zuwa Makaranta dan Samar musu da ilimi, da sana’an yi. Dan kau da talauci cikin matasa da sauran kalubale.

In an Samar da Hukumar, Hukumar zata kasance Mai bada horoswa na sana’ar hannu wa yara da samari da almajirai. Dan kau da talauci da laifuka a kasan.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Bayan hira da manema labaran mu ran lahadi, wanda ya jagoranci tsai da dokar, kakale ( PDP Sokoto), ya ce shugaban kasa ya sanya hanu kan dokar yayin da yara suke murnan bikin ranar yara.

Ya bayyana sanya hannun a matsayin kyauta ne wa yaran Najeriya.

“Muna matukar godiya wa shugaba Muhammadu Buhari Da jajircewa dan yin abinda yake da kamar Mai wuya cikin mutum miliyoyi a matsayin kyauta wa yaran Najeriya.

“Muna taya murna wa jiga jigan da yan kasa dan cin ma wannan burin dan kawo adalci, gaskiya da kuma hadakaiyar mutane a fannin ilimi saboda yaro ko Almajiri ne bare rasa ba a Najeriya”.

Dokar ta samu kiyayya daga wurin mutane da sassa daban daban na kasar tunda aka fito da ita, ta wuce ta samu amincewar majalisa har zuwa saka hannun shugaban kasa.

Daily trust ce ta rawaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button