Labaran Yau

Tinubu Ya Sauke Shugabanin Manyan Hukumomi Na Kasar

Tinubu Ya Sauke Shugabanin Manyan Hukumomi Na Kasar

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da marabus na manyan shugabannin hukumomi na Gwamnatin Tarayya, Jami’u da kampanonin gwamnati. Hakan yazo ne da aiwatar da karfin da dokar kasa ta bashi dan cigaban kasa.

Labaranyau ta samu bayanin daga jawabin Willie Bassy Mai magana da yawun Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Wannan Murabus ta shafi manyan masu shawaran gudanarwa na hukumomi wanda dokar kasa Part 1, Section 153 (i) na 1999 ta tsara, wanda aka gyara na gwamnatin tarayya” a cewar sa.

“Duba da cigaban, Sai an nada sabbin shugabannin hukumomi da jami’u da Kuma kampanonin gwamnati, Duk wata rahoto ko bayani wanda ake bawa shugabannin za a kaiwa shugaban kasa ne ta hannun famanet sakatare na kowani fannin ministiri.

“Famanet sakataren zasu bada rahoton ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya zuwa ofishin shugaban kasa, Ministirin da hukumomin Ana bukatar su bada hadin kai wa umarnin da aka gindaya ranar 16 ga watan Yuni shekarar 2023.

“Famanet sakataren zasu bi umarnin su bayyana wa shugabannin hukumomin da ya shafa da gaggawa nan ta ke”.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button