Labaran YauNEWS

Hukuncin Kotun Ya Sake Tabbatar Da Zabin ‘yan Najeriya Na Tinubu Cewar Barau Jibril

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yaba da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPT) ta yanke, inda ta tabbatar da nasarar APC.

Hukuncin Kotun Ya Sake Tabbatar Da Zabin ‘yan Najeriya Na Tinubu  Cewar Barau Jibril

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yaba da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPT) ta yanke, inda ta tabbatar da nasarar APC.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan, Sanata Barau ya kuma nuna farincikin sa da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPT), tare da tabbatar da nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu.

DOWNLOAD MP3

Sanata Barau, a wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da fitar, Ismail Mudashir, ya ce hukuncin da kotun ta yanke ya sake tabbatar da zabin ‘yan Najeriya kan shugaba Tinubu.

Zaman kotun da alkalai biyar karkashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsammani ta amince da zaben shugaban kasa Tinubu a ranar Laraba.

Yayin da ya bukaci kowa ya amince da sakamakon kotun, ya ce ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da bambance-bambancen jam’iyya ba akwai bukatar hada kai da gwamnati mai ci domin tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta.

DOWNLOAD ZIP

“Hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke kan zaben shugaban kasa ya sake tabbatar da zaben wadanda suka fito a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, don zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasarmu. Yanzu lokaci ya yi da kowa zai hada kai da Shugaban kasa don magance matsalolin kasar nan yadda ya kamata domin amfanin kowa,” inji shi.

Ya kuma nanata kudurin majalisar na samar da dokoki don tallafawa ayyuka daban-daban na bangaren zartaswa da ya dace da ajandar kawo gyara da tsaruka na Shugaba Tinubu.

“A namu bangaren, kamar yadda shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya tabbatar, za mu fito da wasu dokoki da suka dace domin tallafa wa bangaren zartarwa domin magance kalubalen da al’ummarmu ke fuskanta. Za a ci gaba da yin wannan aiki tukuru domin amfanin kowa da kowa,” in ji Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button