Labaran YauNEWS

Tsohon Shugaban Kasa Buhari Yace Nasarar Tinubu A Kotu Nasara Ce Ga Dimokradiyya

Tsohon Shugaban Kasa Buhari Yace Nasarar Tinubu A Kotu Nasara Ce Ga Dimokradiyya

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke na tabbatar da nasarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC)…

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke na tabbatar da nasarar jam’iyyar APC da dan takararta, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Tsohon shugaban kasar a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce kotun kolin ta PEPC ta ajiye tarihi ta hanyar rufe kunne da tayi daga zage-zage da tsoratarwa da duk wani nau’i na son zuciya kuma ta tabbatar da adalci bisa doka ga galibin ‘yan kasar wadanda burinsu shi ne zabin da suka yi shi ne ya cancanta.

“Nasarar kotu a yau, nasarar dimokuradiyya ce da kuma jama’a,” in ji shi “dangane da hukuncin na Kotun Koli, lokacin zabe ya ƙare kuma lokaci ya yi da za a saka maganar rashin yadda da zabe da ma wasu abubuwan na tsana a baya. Daga nan ya kamata sabuwar gwamnatin APC karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta samu goyon bayan kowa domin ganin ta cika alkawuran da ta dauka wa al’umma.”

Buhari ya kuma nuna jin dadinsa ga daukacin ‘yan kasar kan yadda suke wanzar da zaman lafiya a tsawon wannan lokaci tare da addu’ar samun ci gaba dorarre a gwamnatin APC.

Ya mika sakon taya murna ga shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa da jam’iyyar All Progressives Congress bisa nasarar da suka samu a kotu, yana mai musu fatan alheri na ganin sun cika burin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button