Ina Zan Je Cewar Malami kan Zargin EFCC
Tsohon ministan shari’a Abubakar Malami ya karyata zargin da ake mai na rashawa da Kuma zargin yana gudu.
Lokaci kadan bayan dakatar da Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa wanda shugaban kasa Bola Tinubu yayi. Shafin zumunta sun yayata cewa Malami ya bar kasar dan gudun kame.
Bayan magana da Daily Trust ran Alhamis da yamma, Yace shi bai samu takardan ziyara daga ofishin EFCC ba.
A bayanin shi, bayan wanda aka yayata a yanan gizo, yace shi bai fita kasar ba.
Yace “ Ba a nemeni daga EFCC ba ko wata Hukumar yaki da cin rashawa ba. Ina kasar a Najeriya kuma Zan halarci Daurin Aure a kano 2:30 na rana a masallacin Sheikh Isiaka Rabiu a garin Kano Gobe jumma’a.
“Bani da niyyan barin kasan nan, Kuma Zan halarci Duk wani gayyatan da aka min daga duk wani Hukumar gwamnati. Ni dan Najeriya ne kuma na yarda da frojet din Najeriya.
“Zan bada kaina wa gwamnati Najeriya da Hukumar ta.”