Labaran Yau

Hukumar Jami’a Na Kasa Ta Bada Lasisin Bude Jami’un Karatu Biyu Wa Farfesa Gwarzo

Hukumar Jami’a na kasa ta bada Lasisin bude jami’un karatu biyu wa Farfesa Gwarzo

Hukumar jami’an kasa NUC ran jumma’a ta Bada lasisin bude jami’ar canada na Najeriya a Abuja, da jami’ar Franco-British na Kaduna.

Gwamnatin Tarayya ran 15 ga watan mayu ta amince da bude jami’an karatu guda biyu na farfesa Adamu Gwarzo.

An bada lasisin wa mai Makarantun a wani bikin da akayi a babban ofishin Hukumar jami’an kasa NUC a Abuja.

Yayi magana bayan karbar lasisin, Mista Gwarzo wanda yake da jami’ar Maryam Abacha na Najeriya da Nijar. Ya bayyana cewa zai yi kokari wajen bin dokar da Hukumar NUC ta gindaya masa dan bada ilimi Mai inganci.

Ya yabawa Gwamnatin Tarayya na bada lasisin jami’un guda biyu, Yace hakan ya nuna yarda da gwamnati take da shi akan shi.

Shugaban Hukumar NUC Farfesa Abubakar Rasheed, ya taya mai Makarantar murna wajen samun cigaban.

Yace Hukumar ta kawo dokokin da zata taimaka wajen gudanar da Jami’un da ba na gwamnati ba, hakan zai taimaka wajen kawar da kalubalen da jami’un suke fuskanta a kasar.

Bisa hakan, Shugaban jami’ar Maryam Abacha Farfesa Mohammad Israr, ya taya wa ciyaman na
Kakakin Makarantar murna wajen samun wannan cigaba.

A wajen taron, Mista gwarzo ya halarci wajen tare da na tsare tsaren karatu na MAAUN Na Najeriya, Dakta Nura A. Yaro da sauran Jami’ai na jami’ar.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button