Labaran Yau

Hukumar NEMA Ta Bada Agaji Ga Mutane 23,000 Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Niger

DOWNLOAD MP3

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa NEMA, ta bayar da tallafin kayan agaji ga manoma 23,000 da kuma marasa galihu da ambaliyar ruwa ta 2022 ta shafa a jihar Neja.

Babban daraktan hukumar ta NEMA, Alhaji Mustapha Ahmed ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da shirin rabon kayayyakin a garin Minna a karshen mako. Ahmed, wanda ya samu wakilcin mai kula da rabon kayayyakin, Alhaji Abubakar Yusuf, ya ce an dauki matakin ne don tallafa wa manoman da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2022 da kuma wadanda suka fi fama da raunana don dakile illar bala’in.

Ya ce, “Ku tuna cewa abin bakin ciki na bala’in ambaliyar ruwa na 2022 ya shafi al’ummomi da dama a fadin kasar nan ciki har da jihar Niger. Wannan yunkuri na “Taimakon Gaggawa na Tattalin Arziki na Musamman na Kasa da Rayuwa.

Ya bukaci masu cin gajiyar da su yi amfani da kayan yadda ya kamata don inganta yanayin zamantakewa da tattalin arzikinsu. A wani sako da ya aike mataimakin gwamnan jihar Neja, Kwamared Yakubu Garba, ya yabawa hukumar ta NEMA bisa wannan daukin da aka yi, inda ya kara da cewa za ta kawo dauki ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

DOWNLOAD MP3 HERE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button