
Wani matashi ya fito shafin zumunta na twitter ya yi gargadi mai zafi zuwaga shahararrun yan kannywood
Wato matashin dai abun yayi masa zafi sosai irin yadda y wasu abubuwa ke gudana tsakanin yan siyasa da yan kannywood din, ya wallafa rubutun ne a kafar sada zumunta na twitter.
Matashin meh suna Na Biyar ya wallafa wannan rubutun ne inda yake kira da gargadi ga duk wani wanda hake jin kansa celebrity ne a Masana’atar Kannywood inda yake cewa.
“Zuwa ga Celebrities ɗin masana’antar #Kannywood, muna jan hankali a gareku cewa, a cikin ku duk wanda ya karbi kudi ya tallata mana ɗan takara ya san bai cancanta ba daga baya kuma aka shiga masifa a ƙasa yazo yana wayar da kan mutane cewa a koma ga Allah to sai ya ci uwarsa”
Zuwa ga Celebrities ɗin masana'antar #Kannywood, muna jan hankali a gareku cewa, a cikin ku duk wanda ya kabi kudi ya tallata mana ɗan takara ya san bai cancanta ba daga baya kuma aka shiga masifa a ƙasa yazo yana wayar da kan mutane cewa a koma ga Allah to sai ya ci uwarsa 📌
— Na Biyar (@Na_Biyar) February 22, 2023