Labaran Yau

Zan Cigaba Da Korin Ma’aikata Da Rushe Gine Gine Cewar El-Rufai

Zan cigaba da korin Ma’aikata da rushe gine gine cewar El-Rufai

Gwamnan Jihar kaduna Nasir El-Rufai, yayi alkwarin cire mutanen da basu dace ba a gwamnati, da rushe gine ginen da akayi ba bisa ka’ida ba har zuwa karshen lokacin sa.

Gwamnan wanda yake da kasa da kwana bakwai a karagar mulki, ya bayyana hakan a wajen kaddamar da littafin sa akan gwagwarmayansa.

Sunan littafin sanya mutane a farko (putting the people first), wanda Dan jarida Emanuel Ado ya rubuta.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Ya ce “Duk wani mummunan abu da muka gani, Zamu cire dan sabon gwamna ba sai yayi ba. Ku kalli yadda zamuyi Kamin karshen lokacin da Zamu bar ofishi. Zamu kori duk wanda bai dace ba kuma zamu cire mummunan abubuwa”.

Gwamnan yace a yanzu kamin ya sauka ya karbi gine gine guda tara wanda ke sunar Ahmed Makarfi tsohon gwamna na jihar Kaduna, kuma ya amince dan rushe su.

Bayanin shi a wajen taron, Gwamna Nyesom Wike ya bayyana shi gwamna akan shi ba Mai tsoro bane wanda ya iya magana a Najeriya.

Wike yace wanda suke iya fadin gaskiya da karagar mulki a kasar Suna da wuyan gani.

Wike yace “Elrufai a wajena shugaba ne, Kuma dattijo ne mai hali da kwazo, jajircewa da kuma hukunci na gaskiya da adalci.

“Kuma mutum ne wanda baida girmama ka’idojinsa, kuma bayi raina wasu ko tazarci dan yaci ribar wani abu. Ina tuna lokacin da ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika wanda ya nuna cewa yakamata yayi abinda mutane suke bukata dan kar ya juya hagu a tarihi.

“Bansan gwamnoni nawa ne zasu iya rubuta wa shugaban kasa wasikar ayi abinda yakamata a jam’iyya daya ba. Akan cewa kar a fadi hagu a idon tarihi.

Wike ya bada kyautan miliyan 20 a wajen taron, shugaban kasa mai jiran gado Bola Tinubu ya samu wakilci daga tsohon shugaban tetfund kashim Imam wanda ya bada kyautan miliyan 20 shi ma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button