Labaran Yau

Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Biliyan 57 wajen horar da Malamai – UBEC

Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Biliyan 57 wajen horar da Malamai – UBEC

Hukumar kula da Ilimi Firamare UBEC, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bada kudade kimanin naira biliyan 57 wa jihohi dan horar da Malamai a shekara goma sha uku.

Shugaban Hukumar, Dakta Hamid Bobboyi ya bayyana hakan a wajen taron kasa akan horaswa ta Malamai a Abuja ranan litinin.

Taron da akayi mai suna: “cigaban Malamai a Najeriya dan samun ingancin karatun Firamare”.

Bobboyi ya yabawa gwamnatin tarayya dan inganta ilimi a wannan fannin.

Ya kara da nuna cewa kadan daga cikin Malamai ne suka horaswan a shekarun da suka gabata, yayin da ya kalubanci gwamnoni da suyi abinda yakamata dan inganta ilimi wajen horar da Malamai.

“Bincike da UBEC tayi na 2022, ta bayyana cewa kashi 67.5 cikin dari na malaman Makarantun gwamnati da malamai kashi 85.3 cikin dari na makarantun Firabet basu samu horaswa ba bayan sun fara koyarwa ba a shekara biyar daga 2018 zuwa 2022.

“Kuma wannan al’amari ta taimaka wajen dukufewar ilimi Mai inganci.

“Gwamnatin tarayya ta bada ta hannun UBEC, Kudi naira Biliyan hamsin da bakwai miliyan dari da sittin da biyar, dubu dari bakwai da hamsin da daya da dari hudu da sha biyar da kobo sha biyu dan taimakawa jihohi wajen horar da Malamai daga shekarar 2009 zuwa 2022.

“Wanda hakan bare horar da Malamai duka ba amma jihohin da ake taimakawa sun saka ido ne akan kudaden gwamnatin tarayya kuma basu kari wajen bunkasa horaswan malamai.” A cewar sa.

Ya ce wannan matsala ita ke kawo faduwa ta ingancin ilimi na Firamare.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button