Chelsea Sun Kammala Sayan Gola Djordje Petrovic Akan Kudi £14m
Petrovic zai nemi waje a Chelsea shida Robert Sanchez bayan tafiyar Edouard Mendy da Kepa Arrizabalaga daga Chelsea.
Petrovic
Robert Sanchez
Petrovic ne gola na biyu da Chelsea suke son saya bayan Robert Sanchez da suka saya daga Brighton akan kudi £25m saboda tafiyar Kepa Arrizabalaga loan zuwa Real Madrid da kuma da kuma sayar da dayan golan su Edouard Mendy dasuka yi zuwa Al-Ahli.
Kepa
Mendy
Dan wasan Petrovic me shekara 23, gola ne me kokari, saboda yayi nasarar hana cin kwallo a wasanni 22 daya buga wannan season din a Major League Soccer.
Petrovic yace “kama gola a Premier League kamar mafarki neh a wajen sa” sannan kuma gashi zai kama gola ne a Chelsea, daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa.