Labaran YauNEWS

Yan kasuwa A India Sun Zuba Jarin kudi Har Dala Biliyan 14 A Najeriya

Yan kasuwa A India Sun Zuba Jarin kudi Har Dala Biliyan 14 A Najeriya

A jiya Laraba, Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa masu zuba jari na kasar Indiya bisa gagarumin kudirin da suka yi na kusan dala biliyan 14 a yayin taron tattaunawa da shugabanin Najeriya da Indiya a birnin New Delhi na kasar Indiya. Ya jaddada cewa Najeriya a shirye take ta ba da mafi kyawun riba kan zuba jari, wanda hakan muna fata ya jawo hankalin masu zuba jari. Shugaba Tinubu ya yi maraba da zuba jari da yan kasuwar suka yi niyyar yi, ciki har da alkawarin fadada dala biliyan 8 da kamfanin Indorama Petrochemical Limited da daya daga cikin masu zuba hannun jarin yayi, don samar da takin zamani da kuma kayan aikin sarrafa man fetur a Eleme, jihar Ribas.

Bugu da kari, Jindal Steel and Power Limited, wani fitaccen mai samar da karafa mai zaman kansa a kasar Indiya, ya tabbatar da zuba jarin dala biliyan 3 a Najeriya, bayan tattaunawa da shugaba Tinubu a yayin taron G-20 a birnin New Delhi. Mista Jitender Sachdeva, wanda shi ne Shugaban Kamfanin SkipperSeil Limited da yayi fice a fadin duniya, ya sanar da cewa zai zuba jarin dalar Amurka biliyan 1.6 wajen kafa tashoshin samar da wutar lantarki megawatt 100 a fadin Arewacin Najeriya, tare da kara 2,000MW na wutar lantarki a cikin shekaru hudu masu zuwa, sannan mai kamfanin ya rattaba hannu kan takardar yarjejeniya da fahimtar juna tsakanin sa da gwamnatin Najeriya a matsayin sa na shugaban kamfani mai zaman kashin kansa.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Bugu da kari, shugaban kasar ya amince da wata sabuwar yarjejeniya ta dalar Amurka biliyan 1 don bunkasa masana’antun tsaron Najeriya (DICON) don samun wadatar kashi 40% na samar da kayan aikin tsaron cikin gida nan da shekarar 2027, tare da hadin gwiwar Shugaban masanaantar makamai na Sojoji da Masana’antu na Gwamnatin Indiya.

Fitaccen kamfani na Indiya mai suna Bharti Enterprises da ke kasuwanci a sassa daban-daban, ya bayyana kudirinsa na zuba jarin karin dala miliyan 700 a Najeriya, kuma ya dauki alwashin aiwatar da na shi zubin kudin nan take.

Shugaba Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatin sa na mayar da hankali wajen mayar da wadannan kudaden na yarjejeniyoyin zuwa matakin da zasu kawo dauki da burunkasa a masana’antu wanda zasuyi aiki da kuma samar da ayyukan yi a Najeriya. Ya ja hankalin masu son zuba jari da kada su yi kokonto, ya kuma ba su tabbacin niyyar jagorancin sa na bada sakamako ta hanyar da ta dace kuma akan yarjejeniyar da aka kulla.

Ya jaddada cewa Najeriya na ba da damammakin kasuwanci da saka hannun jari a nan gaba, wanda jarin da za’a zuba zai samu goyan bayan aiki tukuru da zai bada ingantattun sakamako kuma da cimma manufofin tattalin arziki kuma ya dau alwashin bada jagoranci mai nagarta.

Shugaban ya tabbatar da rawar da yake takawa wajen jagorancin sa da kuma ba da himma wajen nemo hannun jari, wadda ake fatan ya kawo ci gaba, da wadata ga dimokuradiyya mafi girma a Afirka, inda ya bayyana yadda Najeriya ta fara samun ci gaba a harkokin kasuwanci wanda ke da alaka da ma’aikatan sa masu kishin ci gaban kasa, da kuma Muradin samun nasarar gwamnatin da ya fara jagoranta watanni uku da suka wuce, kuma wannan yunkuri nasu shiri ne na ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba.

Bugu da kari, shugaba Tinubu ya nuna farin cikinsa kan yadda kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya ta taka rawar gani a zamaninsa.

Mista Wale Edun, Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, ya nuna godiya ga Mr. Naveen Jindau, shugaban kamfanin Jindal Steel and Power Limited, bisa sabon jarin da suka zuba na dalar Amurka biliyan 3 a fannin sarrafa karafa a Najeriya a yayin taron. Tattaunawa mai taken “Gina Haɗin gwiwa tare da Sabbin matakai don Samar da Tattalin Arziki Daban-daban da wadata a kasar Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button