Labaran Yau

Abba Gida Gida Zai Yi Duba Ga Dalilan Cire Sunusi A Sarautar Kano

Abba Gida Gida zai yi duba ga dalilan cire Sunusi A sarautar Kano

Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Jagoran yan kwankwasiya, Rabiu Musa Kwankwaso yace gwamna Mai jiran gado na jihar Kano zai yi duba da dalilan da yakai ga cire Alhaji Muhammadu Sunusi a kujerar a matsayin Sarki na sha hudu a tarihin masarautar Kano.

Sunusi yazama sarki a matakin kwankaso na karshe na gwamnan Kano, wanda ganduje ya tube mai sarautar bayan ya zama gwamna bayan sunusi yazama sarki yana mataimakin gwamna.

An cire Sunusi ran 9 ga watan maris a shekarar 2020, Kuma aka koreshi daga garin zuwa Loko Zuwa Awe a jihar Nasarawa.

Ganduje ya raba masarautar zuwa kashi biyar, bisa hakan aka nada sabbin sarakuna.

Maganar da yayi a wata bidiyo,kwankwaso yace za ayi duba da dalilan cire Sanusi a matsayin na sarkin kano, gwamnatin Abba Kabir Yusuf zatayi abinda ya kamata.

“Munyi kampen kuma ansan yanda muka sanu a jihar Kano da Najeriya. Zamu cigaba da aikin mu masu kyau daga inda muka tsaya. Wannan sabon gwamna da mukarrabansa zasuyi abinda ya dace”

“ A matsayin mu na manya, Zamu cigaba da basu shawarwari suyi abinda ya dace, bamuyi kokarin cire wani ko hana cire wani ba, amma yanzu dama ta samu.

“Wanda aka basu daman zasu zauna Kuma sugani yadda zata kasance, kuma abinda ya kamata suyi. Shi sarkin da masarautar an raba ta kashi biyar. Shugaba yakan gaji Mai kyau, Mara kyau da wasu lamari wanda ke da wuyan gyarawa”.

Ya Kuma roki Allah da ya taimaka musu da sabon gwamna wajen yin abinda ya dace cikin sauki.

 

Babu Nadama cire Sunusi A sarauta

Shekara daya bayan cire Sunusi a karagar sarauta, Ganduje yace ya dau matakin cire shi ne dan ya taimakawa masarautar daga cin zarafin da zai iya mata.

Ya ce a wajen fitar da littafin Goodluck Jonathan wanda dan jarida Mista Bonaventure Melah ya wallafa.

Ganduje ya bayyana cewa Sunusi bai cancanta wa sarauta ba, Yace cire zaman Sunusi sarki anyi ne a batawa Tsohon Shugaban kasa Goodluck.

Jonathan ya cire Sanusi a matsayin gwamnan bankin tarayya saboda bayyana satar kudi dala biliyan 49 wanda wasu sukayi a karkashin mulkin sa.

Laifin sunusi shine da ya fadawa Jonathan laifin a boye Sai yasa ayi bincike da yafi.

“Jonathan yayi jarumta wajen cire Sanusi a gwamnan bankin tarayya, wanda ya jawo masa bakin jini. Da Sanusi yace an sace dala biliyan 49 a mulkin Jonathan, Nace a raina da ya fada masa a boye.

“Da ka bashi kofofin bincike Kamin wanda suka sace suyi tunanin boyewa.

“A bayanin yace, abinda ya yayi babu dattako, bayanin ya kawo bakin jini”

Yace an daura shi a kujerar ne dan a nuna wa Jonathan cewa mutan kano suna sanshi Kuma badan ba wanda ya yafi kowa cancanta ba, hasali ma bai cancanta ba.

Sai yasa muka bashi maganin Jonathan bayan Mun karbi mulkin gwamnatin kano cewar Ganduje.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button