Yanzu Babu Kasar da za tayi kasadar Zuba Hannun jari a Nageriya duba da yadda Gwamnatin tarayya tayiwa matatar Man Dangote Atiku Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya koka matuka kan yadda Gwamnatin tarayya ke kokarin dakile kamfanin rifainarin Dangote.
Mataimakin yakara da cewa lallai rikicin da ke tsakanin Aliko Dangote da NMDPRA yana da ban tsoro da matuka.
Matatar mai ta Dangote shine babbar jarin kasa tamu mai zaman kanta, yana da matukar muhimmanci idan muka tallafa wajen darajashi da kwanciyar hankali a Najeriya.
Matatar mai meh karfin bpd 650,000 na da matukar muhimmanci ga bukatun makamashi da kwanciyar hankali a tattalin arzikinmu.
Kuma ita jarin da NNPCPL ta yi ya nuna muhimmancinsa kwarai dagaske. Idan muka yi sakaci da wannan, za mu yi kasadar dakile muhimman masu saka hannun jari na ketare kai tsaye.
Babu wani mai saka hannun jari da zai aminta da al’ummar da ke lalata manyan kadarorinta.
Kare manyan saka hannun jari irin na Dangote yana da mahimmanci don jawo hankalin FDI da haɓaka haɓakar tattalin arzikinmu.
Cewar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.
Jiya litinin 22 ga watan yuli Ƙaramin Ministan Man Fetur ya jagoranci zaman tattaunawa da Alhaji Aliko Ɗangote da sauran masu ruwa da tsaki kan harkar man fetur a Najeriya dangane da taƙaddamar da ke faruwa kan kasuwancin man fetur ɗin.
Ga Bidiyon Interview Din Aliko Dangote