Labaran Yau

Bidiyon Haduwar Rarara Da Ganduje A Abuja Yayin Dasuka Kaiwa Bola Tinubu Ziyaran Maraba

Haduwar Tinubu da Rarara a Abuja ya janyo samun maslaha tsakanin mawakin dan siyasa da gwamnan Kano

Jarumi mawakin siyasa, wanda yayi fice a wakokin yaba siyasa a Arewacin Najeriya da kasa gaba daya, Dauda kahutu Rarara, ya kaiwa Shugaban kasa Mai jiran gado Bola Ahmad Tinubu ziyara a garin Abuja bayan dawowansa.

Shugaban kasa mai shigowa ya fita yawon shakatawa a duniya bayan lashe zaben shugaban kasa da ya gabata a kasar Najeriya.

Bola ya fita Najeriya inda ya fara zuwa Paris a kasar faransa na wani lokaci wanda ya wuce landan a kasar turai yayin da ya shirya zuwa saudiya dan yin ramadana da umrah.

Tinubu ya dawo kasar kwanaki kadan da suka wuce, Rarara ya sake waka yana lala marhaban wa Shugaban kasa Mai shigowa da “baba ya dawo da kwari”

A wakar yake bayyana cewa an kona mai gida da gona dan baba Ahamadu bola bayi nan… yana mai kararsu cikin wake.

Jita jita a kafafen sada zumun ta suna zargin gwamnan jihar kano Abdullahi Ganduje yake yin hakan dan bayi bayan dan takarar APC a matakin gwamna.

Bayan Rarara ya nuna goyon bayansa wa dan majalisan tarayya Sha’aban Sharada a takarar gwamnan Kano.

Ana zargin matsalolin da suka haifar da hatsaniyan dake tsakanin Ganduje da Rarara.

Amma bisa yanda muka gani a sabon bidiyon dake zaga kafafen zumunta a halin yanzu an samu maslaha tsakanin shi Ganduje da Dauda Kahutu Rarara.

Ga Bidiyo 👇

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button