Labaran YauNEWS

Kashi 99 Na kuri’un Mutanen Kogi Muka Zo Nema – Ganduje

Kashi 99 Na kuri’un Mutanen Kogi Muka Zo Nema – Ganduje

Abdullahi Ganduje, Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bukaci ‘yan jihar Kogi da kada su baiwa jam’iyyar goyon baya da kuri’u kasa da kashi 99 cikin 100 na nasara a zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ganduje ya bayar da wannan umarni ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar da magoya bayansa a wajen bukin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar na kasa da na Jihohi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

DOWNLOAD MP3

“A yau muna kaddamar da kwamitin yakin neman zabe na jiha a hukumance wanda zai hada hannu da kwamitin yakin neman zabe na kasa da kuma kwamitocin yakin kananan hukumomi domin ganin an samu nasara a zaben.

“Kun gwada kyakkyawan shugabanci daga gwamnatin Gwamna Yahaya Bello kuma a matsayinmu na jam’iyya muna fatan za mu kara yin aiki da mai rike da tutarmu, Alhaji Usman Ododo, da zarar an zabe shi.
“Ododo ba boyayye ba ne, wanda kuma shi mutum ne mai aminci kuma mai aiki tukuru wanda a shirye yake ya yi mana hidima da jiha a matsayin gwamna.
“Ba mu sa ran kuri’u kasa da kashi 99 cikin 100 na nasara daga mutanen Kogi a zaben gwamnan da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba,” in ji shi.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button