Labaran YauNEWS

Gwamnatin Tarayya Zata Zauna Da Kungiyar Kwadago Ranar Litinin

Gwamnatin Tarayya Zata Zauna Da Kungiyar Kwadago Ranar Litinin

A kokarinta na dakile yajin aikin jan kunne na kungiyar kwadago ta Najeriya da ta shirya yi a ranakun Talata da Laraba, gwamnatin tarayya ta ce a shirye ta ke ta gana da kungiyar kwadago a ranar Litinin mai zuwa.

Sai dai kungiyar kwadagon ta ce babu gudu babu ja da baya a yajin aikin jan kunnen na kwanaki biyu, duk da cewa ta ce a shirye take ta tattauna da gwamnati duk da saba alkawuran da ta dauka a baya.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ya ce: “Tabbas, muna fatan za a iya dakile yajin aikin da kungiyar take da niyyar shiga.
Har yanzu suna tattaunawa kuma sun fara fahimtar matsayin juna. Za su sake haduwa a ranar Litinin.

Kun san cewa sabon Ministan ya shigo yanzu kuma ya fara hulda da kungiyar NLC. Ci gaba, za ku ga ƙarin haɗin gwiwa tare da ƙungiyar ma’aikata. Ya zuwa yanzu, tashin hankali ya ragu amma har yanzu ana ci gaba da aiki. Zuwa ranar litinin za su sake haduwa kuma da fatan za a cimma matsaya cikin lumana kan lamarin.”

Dangane da abin da gwamnatin tarayya ke shirin yi dangane da yajin aikin na kwanaki 21 da ta shirya farawa nan gaba a cikin wannan wata idan bangarorin suka kasa cimma matsaya, ministan ya bayyana yakinin cewa za a shawo kan lamarin kafin lokacin.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan ne ya sa na ce muna kokarin samun matsaya guda don dakile yajin aikin da ke gabatowa. Da zarar an samu haka, to sai a ci gaba da wata tattaunawar daga bisani”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button