Labaran Yau

Wani Mutum Yataba Nacemin Kaman Ya Ka***She Kanshi Akaina Amma Walhy… Jamila Ibrahim

Na Kalli full video din hirar wannan yarinyar Kuma wallahi na tausaya mata sosai – Jamila Ibrahim

Malama Jamila Ibrahim tadanyi tsokaci gameda labarinda yar wasan Kannywood Rakiya tayi gameda Soyayyar dake damunta.

Wanda Bai taba fadawa soyayya Mai karfi ba bazai gane abunda takeji ba šŸ„ŗ, sai dai muyi mata fatan samun waraka …

Naga wasu na cewa saurayin Bai kyauta ba ta Yaya yarinya na mugun sonka ka kasa aurenta šŸ˜ž

DOWNLOAD HERE

Uhm wallahi lamari na aure da soyayya akwai rikitarwa wallahi idan ka Daina son mutum ko duniya za’a dau a baka bazaka iya rayuwa dashi ba …

Kila lokacin da suke soyayya ita ke sonshi , shi kulata yakeyi Dan bashida wacce ya kamu da sonta a lokacin , na tabbata da ace yanda take sonshi haka yake sonta Babu yanda za’ayi Bai aureta ba …

Namiji idan Yana son mace ko sama da kasa zasu hadu bazai Daina sonta ba , mu mata ne ma muke siyar da soyayyar mu akan abun duniya…

DOWNLOAD MP3 HERE

Muma da muketa ganin saurayin Bai kyauta wallahi akwai mutane dayawa da ko zasu dauki duniya su bamu bazamu iya aurensu ba ,Koda mun karbi duniyan a hannun wannan mutumin sai dai ayi sha’ani kawai amma Babu soyayya..

Ni kaina lokacin Ina secondary school wani mutumi ya taba nacemun kaman ya ka**she kanshi a kaina amma wallahi ban tabajin Ina sonshi ba , Kai har babana ya bashi ni an karbi Goron tambayar Aurena dashi wallahi dukda hakan bana kaunar sa …

Nayi nayi in koyi son mutumin wallahi na kasa , idan Na ganshi sai inji duk farincikina ya Kau , har yau har gobe da zance masa ya aureni a shirye yake amma kuma na gwammace na auri wani ba shi ba šŸ˜­

Kunga kuwa shi so ba’a masa dole , wani halitta ce ajiyayye jikin Dan Adam idan ka hadu da Wanda Kaji wannan halittar taka da nasa yazo Daya toh shine soyayyar ke Dadi šŸ‘Œ

Allah ya hada kowa da Wanda yakeso itama ta sonsa , da Wanda kikeso yake sonki…

Munawa rakiya fatan samun waraka ,idan kuma Wanda takeson Alkhairi ne Allah ya batashi cikin saukišŸ‘

Daga Jamila Ibrahim

Ga Hiran Hadiza Gabon Da Rakiya ā‡“

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button